Iran ta bayyana cewa zargin kasar da hannu a yunkurin hallaka Donald Trump kage ne da rashin-ta-fadi kawai.
Da yake mayar da martani kan zargin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da ” labarin da ya danganta da na kage” na yunkurin kisan gillar da aka yi wa Trump.
Araghchi ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, kwana guda bayan da ma’aikatar shari’ar Amurka ta yi ikirarin cewa Iran ta goyi bayan yunkurin kashe Trump makonni kadan kafin zaben shugaban kasar na ranar 5 ga watan Nuwamba.
Ya kara da cewa “Al’ummar Amurka sun yi zabe kuma Iran na mutunta ‘yancinsu na zaben shugaban da suke so.
Yayin da yake ishara da kisan gillar da aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Tehran sa’o’i kadan bayan da ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, wanda kowa ya san way a aikata shi, Araghchi ya nuna cewa zargin da ake yi wa Iran na yunkurin kashe Trump a daidai lokacin da aka zabe shi an yi ne da wata manufa.
Tunda farko dama kakakin ma’aikatar wajen Iran Ya yi kalamai irin hakan inda ya bayyana rahoton da wata mummunar makarkashiya da kungiyoyin yahudawan sahyoniya da masu adawa da Iran suka shirya da nufin kawo cikas ga alaka tsakanin Amurka da Iran.
A baya-bayan nan ne ma’aikatar shari’a ta Amurka ta shigar da karar Farhad Shakeri, wani dan kasar Afganistan, wanda ake zargin dakarun kare juyin juya hali na Iran da kitsa masa yunkurin kisan gillar da aka yi wa Donald Trump gabanin zaben shugaban kasa.