Qatar Ta Ce Ta Dakatar Da Kokarin Shiga Tsakanin Isra’ila Da Gaza

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta ce ta dakatar da kokarin shiga tsakani domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza. Matakin na zuwa ne a

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta ce ta dakatar da kokarin shiga tsakani domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna takaicin rashin samun ci gaba kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.

Qatar ta ce ta dakatar da kokarinta na shiga tsakanin Hamas da Isra’ila har sai bangarorin sun nuna da gaske  su ke wajen kokarin da ake na kawo karshen yakin Gaza.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar X, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Majed al-Ansari ya ce Qatar ta sanar da bangarorin da abin ya shafa kwanaki 10 da suka gabata game da aniyar ta.

Tun da farko a ranar Asabar, kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito wata majiya ta diflomasiyya tana cewa ofishin siyasa na Hamas a Qatar “bai da wani tasiri “.

Sai dai al-Ansari ya ce rahotannin da ake yayatawa game da ofishin siyasa na Hamas da ke Doha ba gaskiya ba ne, yana mai cewa “mahimmancin ofishin a Qatar shi ne ya zama hanyar sadarwa tsakanin bangarorin da abin ya shafa”.

Wani babban jami’in Hamas ya ce suna sane da matakin da Qatar ta dauka na dakatar da yunkurin shiga tsakani, “amma babu wanda ya ce dasu su fice”.

To saidai wani jami’in Amurka ya ce gwamnatin Biden ta sanar da Qatar makonni biyu da suka gabata cewa ci gaba da kasancewar ofishin Hamas a Doha ba shi da wani amfani kuma ya kamata a kori tawagar Hamas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments