Biden Ya Goyi Bayan Najeriya Ta Samu Kujerar Dindindin A MDD

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana goyon bayansa ga hankoron Najeriya na samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. A yayin wata

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana goyon bayansa ga hankoron Najeriya na samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

A yayin wata hira ta wayar tarho tsakaninsa da takwaransa na Nijeriya, Bola Tinubu, Biden ya bayyana aniyar inganta wakilcin nahiyar Afirka a tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tattaunawar ta dace da muhawarar da ake ci gaba da yi game da wakilcin ƙasashen Afirka a Majalisar Dinkin Duniyar.

“Amurka na da aniyar ganin Afrika ta samu kujerun dindindin guda biyu a majalisar,” a cewarsa.

Fatan Nijeriya na samun kujerar dindindin na nuna dadaddiyar  bukatar kara samun wakilci a harkokin gudanarwar duniya.

A halin yanzu, Afirka na da kujerun karba-karba guda uku a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniyar mai mambobi 15, yayin da a duk bayan shekaru biyu babban zauren majalisar ke zaɓar mambobin da ba na dindindin su biyar na wa’adin shekaru bibiyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments