Tun a daren jiya ne dai sojojin HKI su ka tsananta kai hare-hare a yankunan mabanbanta na zirin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdianwa 25.
A gefe daya, sojojin HKI sun sanar da halakar wani baban jami’insu daga rundunar “Shakid” bayan da ya yi jiyya daga raunukan da ya samu a fada a Gaza.
Sanarwar ta ce, sojan ya sami rauni ne tun a ranar 17 ga watan Satumba tare da wasu sojoji 4, bayan da wani bom ya tashi a cikin wani gini da su ka shiga a garin Rafah.
Kwanaki uku da su ka gabata ma dai rundunar sojan mamayar ta sanar da cewa, wasu manyan jami’ai 3 sun mutu yayin da wani jami’in sojan daya ya jikkata a fadan da ake yi a Jabaliya.
A yau Juma’a rundunar “Sarayal-Quds” ta kungiyar Jihadul-Islami, ta sanar da cewa ta kai hari akan sansanin soja ‘yan mamaya da ke Abu Jarad a gabashin birnin Rafah ta hanyar amfani da makami mai linzami samfurin “ 107”.