Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa a Najeriya ta ba da shawarar dakatar da kudirin yi wa haraji kwaskwarima da gwamnatin tarayya ke shirin yi.
Mambobin majalisar National Economic Council (NEC) sun kunshi gwamnoni ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima.
Da yake magana da manema labarai bayan zaman majalisar a wannan Alhamis, Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya ce sun yanke shawarar dakatar da ƙudirin ne bayan cece-kucen da ya biyo baya “da zummar bai wa masu ruwa da tsaki dama.
Bayan kammala taron da ta gudanar a ranar Lahadi, Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) wadda Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya ke jagoranta, ta ƙi amincewa da shirin kara harajin VAT.
Daga bisani shi ma Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasawara, ya kare matakin da cewa sabon tsarin ƙara harajin zai zamo wata babbar illa ga Arewacin kasar.
Alhamis ne Fadar Shugaban kasa ta ce ta aike wa Majalisar Dokoki ƙudirin gyaran karbar harajin domin amincewa da shi.