Dakarun tsaron saman kasar Iran sun tabbatar da hare-haren da Isra’ila ta kai a yankunan Tehran, Khuzestan da Ilam, inda ta ce an yi nasarar dakile harin.
“Duk da gargadin da jami’an Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka yi a baya ga gwamnatin sahyoniyawa da su guji duk wata takala, wannan gwamnatin ta kai hari a wasu sassan cibiyoyin soji a safiyar yau a wani mataki mai na neman tayar da hankali. ”
Hadin gwiwar tsarin tsaron sama na kasar ya yi nasarar kakkabowa tare da dakile wannan ta’addanci, in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, hare-haren sun haifar da barna kadan a wasu wurare kuma ana gudanar da bincike kan girman lamarin.
Babu wani harin makami mai linzami ko wani tasiri da ya faru a kan cibiyoyin soji na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) a yamma da kudu maso yammacin Tehran, inji sanarwar.
A wani labara na daban kuma Hukumar kula da sufirin jiragen sama ta Iran ta sanar cewa al’amura sun koma daidai kamar yadda aka saba a filin jirgin saman Imam Khumaini da kuma filin jirgin Mehrabad.