Iran Za Ta Halarci Taron Shugabannin Kasasahen “BRICKS” A Karon Farko A Matsayin Cikakkiyar Memba

A gobe Talata 22 ga watan Oktoba ne za a bude taron kungiyar “BRICKS”  a matakin shugabbin kasashen membobi a birnin Kazan na kasar Rasha.

A gobe Talata 22 ga watan Oktoba ne za a bude taron kungiyar “BRICKS”  a matakin shugabbin kasashen membobi a birnin Kazan na kasar Rasha.

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan zai halarci taron a karon farko bayan da kasar ta zama cikakkiyar memba a cikin kungiyar ta tattalin arziki da siyasa.

Taken da aka bai wa taron na wannan lokacin shi ne: “Karfafa juna domin cigaba da tabbatar da tsaro a duniya.”

Bayan ga kasashen da suke membobi a kungiyar da za su halarci taron da akwai kuma wasu shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da sun kai 30 da za su je a matsayin baki, ‘yan kallo.

Bugu da kari wannan taron zai zama wata dama ta yin ganawa a tsakanin shugabannin kasashe domin tattaunawa saboda bunkasa alaka a tsakanin kasashensu.

A farkon wannan shekarar ta 2024 ne dai Iran ta zama cikakkiyar mamba a cikin kungiyar ta BRICKS.

An kafa dai wannan kungiyar ne dai a 2006, kuma mambobinta na farko su ne; Brazil, China, India da kuma Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments