Kissoshin Rayuwa: Sirar Fatimah Azzahra (s) 44

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’aini mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da lattafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na Maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////….Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon Allah(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) da muke mawo muku, mun yi maganar yadda manzon Allall(s) yayi wafati kansa yana jingine a girjin Aliyu dan Abitalib (a), sannan diyarsa Zahra (s) da kuma jikokinsa Alhassan da Alhussain (a) suka kewaye da shi suna kuka.

Jim kadan bayan wafatinsa sahabban manzon Allah daga cikin Ansari suka taru a wani wuri da ake kira sakifa don su zabi shugaba ko khalifan manzon Allah(s) wanda kuma shi ne sa’ad dan Ubadah.

Amma a lokacinda Kuraishawa suka ji labari sai suka yi gaggawa suka zo taron na Sakifa, kuma sune Abubakar, Umar da kuma Abu ubaida dan Jarrah. Sannan a cikin hayaniyar da aka tayar a lokacin sai Umar ya kama hannu Abubakar yayi masa bai’a sannan sauran suka biyu.

Mun kawo maku zancen khalifa na biyu yana cewa: Bai’ar da aka yiwa Abubakar ta bazatace, kuma Allah ya kiyayemu sharrinta. A wani wurin yana cewa wanda ya sake yin  irinta ku kashe shi.

Sannan munji yadda aka yiwa manzon Allah(s) sallar Jana’izi ta musamman, wanda Aliyu dan Abitalib(a) ne ya fara yi masa, kuma kafin haka shi ne ya yi masa wanka ya kuma sanya masa likkafaninsa, wanda shi ne haraminsa na hajjin bankwana. Sannan munn ji yadda aka yiwa khalifa Abubakar bai’a da kuma yadda ya aiki Umar ya je ya fitar da sahabban da suke gidan Aliyu dan Abitalib da Fatimah (s) don su masa bai’a. Da yadda suka kama Zubair dan Awwam, da kuma yadda suka yi bararazanar kona gidan Aliyu da Zahra (a) da duk wanda yake cikinsa, idan basu fito sun yi bai’a ba.

Duka da cewa Fatimah (s) ya ji daga wajen babanta abinda zai faru da ita, amma kuma gani ya kori ji, ta ga al-amarin idanunta. Ta kuma yi mamakin yadda wasu sahabban (s) suka cutar da iyalan gidan manzon All…(s) jim kadan bayan wafatinsa.

A lokacinda suka zo kofar gidan Aliyu (a) suka kuma yi baranar konan gidan, Zahra (s) ta zo kofar gidan ta tana magana dasu, har sai da wasunsu suka gudu daga wurin bayan sun ji muryarta.

Amma wasu tare da khalifa Umar sun kutsa cikin gidan, sun kuma bude ta da karfi, A lokacin Zahra (s) tana bayan kofa sai suka matseta a bayan kofa har sai da kusoshin kofar suka shiga kirjinta, sannan suka jiwa jiririnda ke cikin cikinta rauni, inda daga baya ta yi barinsa.

Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa a lokacinda hakan ya faru tana da ciki wanda tsufarsa ya kai wata shida, na danta mai suna Muhsinu. Manzon Allah (s) ya sanya masa suna tun ba’a haifeshi ba. Daga nan sai suka fada cikin gida, suka kama Aliyu dan Abitalib(a) da karfi saka fito da shi daga gidan. Sai zahra’u (s) ta shiga tsakaninsu da shi sai Umar ya umurci kunfuzu ya daketa da bulalan da take hannunsa, sai ya daketa, inda bulalar ta kewaye hannunta ya kuma kumbura ya tara jini. A wata ruwarai an bayyana cewa Fatimah (s) ta yi kuka tana cewa an kashe jaririna da ke cikina.

Yayan Zahra (s) wadanda suka shaidi yadda aka yi da mahaifiyarsu sun shaida hakan, inda har wata rana daya daga cikinsu wato Imam Alhassan (a) ya yi khuduba yana fadawa Mughiratu dan Shuba a wata majalisa wacce Mu’awiya dan Abisufyan yake cikinta. Yace masa:

‘Kai ka daka Fatimah diyar Muhammad (s) har sai da ta zubar jini, ta kuma zubar da cikinta, kuma ka yi haka don kaskanta manzon Allah(s) da kuma sabawa umurninsa, don kuma keta huruminsa. Hakiki manzon Allah(s) ya fada mata cewa: Kace shugaban matan Aljanna. Na rantse da Allah makomarka – ya kai mughira- wuta ce…har zuwa karshen maganarsa. Wannann kamar yadda ya zo a cikin littafin Ihtijaj shafi na 137 da kuma Biharul Anwar Jz na 43.

A cikin littafin Sulaim dan Qai Al-Hilali yana cewa….Sai Umar ya zo ya daki kofar gidan Fatimah (s) sai yace: ya dan Abitalib ka bude kofa. Da Fatima(s) ta ji haka, sai tace: Ya Umar: me ya sameka ne, baka barimmu da abinda ya samemu? Sai Umar ya ce: Ka bude kofa ko kuma in kona gidan a kanku. Sai ta ce: Ya Umar ba zaka ji tsoron Allah ba, za ka shiga gidana ka shi shi ba tare da izinin na ba?

Sai ya ki ya tafi, da ya ga sun ki budewa sai yace a bashi wuta, sai ya kona kofar gidan da wuta, kofar ta kone tana ci da wuta sai ya turata da kafarsa, Fatimah(s) tana kusa da kofar, ta yi kara, tana cewa ya babana ya manzon Allah. Sai Umar ya bugeta ta gefenta da kan takobin sa, sai tayi kara. Sannan ya daga bulala ya daketa daga saman hannunta, sai ta daga murya tana cewa Ya babana, abinda Abubakar da Umar suka yi a bayanka ya munana.

Sai hadisin ya kara da cewa: Bayan haka sai Aliyu dan Abitalib (a) ya yunkura ya kama wuyar Umar ya kuma juya shi ya kada shi a kasa, ya ji masa rauni a hancinsa da wuyarsa, yayi nufin kashe shi, sai ya tuna da zancen manzon Allah(s) gareshi, na hakuri da abinda zai sameshi, da wasiyar da yayi masa, sai yace masa: na rantse da wanda ya daukaka muhammadu(s) da annabci,   in ba don hukuncin Allah da ya gabata ba, da kuma alkawalin da na dauka wa manzon Allah(s) ba, da ka san cewa baka isa ka shiga gidana ba…..

Sai Umar ya nemi taimako da wasu, sai suka shiga gidan suka cika shi, sai suka yi wa Aliyu (a) taron dangi, suka jefa igiya a wuyansa suka dabaibaye shi. A lokacinda suka yi kokarin fitar da shi daga gidan sai Fatimah (s) ta shiga tsakaninsu ta kofar gidan, sai Kunfuzu ya daketa da bulala, wanda muka ce ya bar alama a hannunta ya kuma tara jini ya kumbura, tana jin zafin wannan dukan har ta yi wafati.

Sannan ya tunkudata ya hadata da bobgo karfi wanda yayi sanadiyyar karya awazanta da sassanta, da haka kuma ta zubar da cikin ta.  Daga rannan Fatima(s) bata gushe ba ba ta da lafiya har ta yi wafati  ko shahada.

Ya zo a cikin littafin Irshadul Kulub, daga Zahra(s) tana cewa: Sun tara itace a kofar shiga gida, don su kona ta su kona mu, sai na tsaya tsakiyar kofa na hadasu da Allah da kuma mahaifina, kan su fita sha’animmu, sai Umar ya karbi bulala daga hannun Kunfuzu, sai ya daki hannu ta, saman zira’i sai ya kumbura ya kuma tara jini, sannan ya tura kofar da kafarsa, ta fada a kaina, ina da ciki, sai na fada kan fuskata, al-hali wuta na cin kofar. Ya dakeni a fuskata har sai da yan kunne na suka fadi, sai nakuda ta zo mani, na zubar da cikin Muhsinu, ba tare da yayi wani laifi ba.

A wani hadisi Imam Sadik (a) yana cewa: … Kuma sababin wafatinta, shi ne kunfuzu bawan Umaru, (wasu suka ce ba bawa bane), ya daketa (s) da kan takobinsa tare da umurninsa, (umar) sai ta zubar da cikin Muhsinu, kuma ta yi rashin lafiya mai tsanani… har zuwa karshen hadisin.

Don haka an ruwaito labarai wadanda suka tabbatar da cewa, fiye da mutum guda ne suka daki Zahra(s) diyar manzon Allah(s) sannan dukan, wani lokaci da kan takobi wani lokaci da kafa wani lokaci kuma da bulala, wanda daga karshe ya kai ga zubar da cikinta (s).

Masu tsara kasidu kuma mawaka da dama sun kawo wannan batun a cikin kisidunsu a duk tsawon tarihin addinin musulunci, inda daya daga cikinsu yake cewa:

Yar Mustafa ta yi barin cikinta, ya bakin cikina-Cikinta wancan da ake kira Muhsinu.

Wani kuma yake cewa:

Da wadanda suka shiga gidan Batulu-Kuma suka nemi zubar da cikinta mai daraja

To masu sauraro saboda kurewar lokaci a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan Allah ya kaimu. wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments