Dakarun “Kassam” Sun Yi Wa Sojojin HKI Kwanton Bauna A Rafah

Adaidai lokacin da yakin Lebanon ya cika kwakani 353, dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun yi wa sojojin mamayar HKI kwanton bauna a yankin Rafah.

Adaidai lokacin da yakin Lebanon ya cika kwakani 353, dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun yi wa sojojin mamayar HKI kwanton bauna a yankin Rafah.

Kwanton baunar na kungiyar Hamas ya dakatar da tafiyar ayarin motocin yakin HKI da suke kai wa ‘yan’uwansu dauki, da hakan ya ja musu asara mai yawa ta rayuka da kuma motoci.

Bugu da kari, dakarun na kungiyar “Kassam’ sun kai hari akan tankar yaki samfurin Mirkava ta hanyar amfani da makamin shuwaz da kuma motar buldoza ta soja samfurin D9.

Tun bayan da HKI ta kutsa da sojojinta cikin yakin Gaza, sojojinta suke fuskantar kai hare-hare daga ‘yan gwgawarmaya a yankin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments