Jordan Ta Yi Allah Wadai Da Kokarin Yahudawan Sahayoniyya Na Rusa Masallacin Al-Aqsa

Kasar Jordan ta yi Allah wadai da kiraye-kirayen da ‘yan mamaya ke yi na kai hare-haren bama-bamai a Masallacin Al-Aqsa mai albarka don tarwatsa shi

Kasar Jordan ta yi Allah wadai da kiraye-kirayen da ‘yan mamaya ke yi na kai hare-haren bama-bamai a Masallacin Al-Aqsa mai albarka don tarwatsa shi

Ma’aikatar Harkokin Waje ta kasar Jordan ta yi Allah wadai, a cikin kakkausar murya kan ci gaba da kiraye-kirayen da kungiyoyin ‘yan nuna wariyar al’umma, masu tsatsauran ra’ayin yahudancin sahayoniyya na haramtacciyar kasar Isra’ila suke yi na neman kaddamar da hare-haren bama-bamai kan Masallacin Al-Aqsa mai albarka da nufin tarwatsa shi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jordan Ambasada Sufyan Al-Qudah A yau Juma’a, ya bayyana cewa: Masarautar Jordan tana jaddada yin watsi tare da yin Allah wadai da wannan mummunar tada zaune tsaye, wadda ta zo daidai da manufar kafa sabbin al’amura a cikin masallacin mai albarka ta hanyar da ta saba wa doka, tsarkinsa da nufin canza yanayin tarihi da na shari’a a cikinsa ta hanyar ci gaba da barin tsagerun yahudawan sahayoniyya suna farma Masallacin Al-Aqsa mai albarka, tare da keta alfarmansa karkashin kariya daga ‘yan sandan gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments