Shugaban Kasar Iran Na Ci Gaba Da Ziyarar Aiki A Kasar Iraki

A ranar farko ta ziyarar tasa, shugaban na Iran ya tattauna da takwaransa na Iraki Abdul Latif, firaminista Mohammed Shi’a Al Sudani da shugaban majalisar

A ranar farko ta ziyarar tasa, shugaban na Iran ya tattauna da takwaransa na Iraki Abdul Latif, firaminista Mohammed Shi’a Al Sudani da shugaban majalisar koli ta shari’a Faiq Zidan a Bagadaza. Ya kuma gana da ‘yan kasar Iran da ‘yan kasuwan Iraki.

Kafin wannan tganawa shugaban kasar Iran da firaministan Iraki, Tehran da Bagadaza sun rattaba hannu kan wasu takardu 14 don fadada hadin gwiwa a bangarori daban-daban na tattalin arziki, kasuwanci, al’adu da zamantakewa.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da firaministan kasar Iraki, Pezeshkian ya yi kira da a aiwatar da cikakken aiwatar da yarjejeniyar tsaron da aka cimma tsakanin Iran da Iraki domin tinkarar ‘yan ta’adda da makiya wadanda suka yi wa zaman lafiya da tsaro a yankin.

Baya ga haka kuma shugaba Pezeshkian ya gana da wasu fitattun ‘yan siyasa na kasar Iraki ad suka hada da Sayyid Ammar Hakim shugaban Tayyar Hikmat, da ma wasyu manyan ‘yan siyasar kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments