shugaban kasar Amurka Donald Trump yace Amurka za ta kawo karshen taimakon da take bawa Iraqi idan ta sake zaben tsohon fira minista Nuri Maliki a matsayin sabon fira ministan kasar, yayi wannan gargadin mai karfi ne a kokarin da ake yi na sake kafa sabuwar gwamnati a iraki.
Trump yayi wannan tsokacin ne a jiya talata kwanaki kadan bayan da jam’iyar dake da rinjaye a majalisar ta bayyana sunan Nuri Almaliki a matsayin dan takararta na mukamin fira minister, kuma ya rubuta a shafinsa na truth social cewa shugaban Amurka yace bagdaza za ta yi mummunan zabi idan ta dawo da nuri maliki
acikin wani bayani da kamfanin dillacin labaran kasar Iraqi ya nakalto ya nuna cewa an riga an yanke hukumci da kuri’u masu yawa da aka kada bayan doguwar tattaunawa da aka yi bisa gogewar nuri al’amliki akan harkokin siyasa da tafiyar da gwamnati da kuma rawar da ya taka wajen daidaita alamuran gwamnati.
Nuri al’maliki yayi mulki a iraki a matsayin fira minista daga shekara ta 2006 zuwa ta 2014 kuma mataimakin shugaban kasa daga shekara ta 2014zuwa ta 2015 yayin da kuma daga shekara ta 2016 zuwa 2018 ya jagoranci bangaren jamiyar Islamic Daawa party political movement.