Loshanko Ya Bayyana Makamai Masu Linzami Samufrin ” Oreshnik” Da Rasha Ta Girke A Bularussia

Shugaban kasar Belarusian Alexander Loshanko ya fada a jiya Litinin cewa; Kasarsa ta amince da girke  makamai masu linzami samufirn ” Oreshnik” guda 10. Dama

Shugaban kasar Belarusian Alexander Loshanko ya fada a jiya Litinin cewa; Kasarsa ta amince da girke  makamai masu linzami samufirn ” Oreshnik” guda 10.

Dama dai tun a ranar 17 ga watan Disamba ne shugaban kasar ta Bularussia ya sanar da cewa; An girke makaman su ne mafi hatsari da Rasha take da su a cikin kasarsa, kuma suna cikin Shirin yaki.

A can kasar Rasha, shugaba Vladrmir Putin ya sanar da cewa, makamin wanda ya fi sauti sauri,kuma mai cin matsakaicin zango, za a girke shi a cikin Shirin yaki a karshen wannan shekarar.

Haka nan kuma Putin  ya lissafo wasu makamai na Rasha wanda ya ce za su bai wa Rasha tsaro  agaban  abokan gaba, da su ne; Makamai masu linzami samfurin “ Burevestnik” mai fika-fikai da ba shi da iyakar Zangon da zai iya ci, da jirgin ruwa mai ninkaya a karkashin ruwa, ” Poseidon” sai kuma jirage marasa matuki.
Putin wanda ya gabatar da jawabi a gaban jami’an ma’aikatar tsaron kasar ta kuma jaddada cewa, kasar tasa za ta ci gaba da kera wadannan makaman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted