Iran Ta Jaddada Cewa: A Shirye Take Ta Tattauna Amma Ba Zata Amince Da Juya Akalarta Ba

Shugaban Majalisar Dabarun Kula da harkokin waje kuma mamba a Majalisar fayyace manufofin kasar Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta tattauna amma

Shugaban Majalisar Dabarun Kula da harkokin waje kuma mamba a Majalisar fayyace manufofin kasar Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta tattauna amma ta kin juya akalarta

Shugaban majalisar dabarun kula da harkokin waje kuma mamba a majalisar fayyace manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kamal Kharrazi, ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta gudanar da zaman shawarwari, amma bazata  amince da dora mata wasu manufofi da suka sabawa muradunta ba.

A wata hira da ya yi da shafin yanar gizo na KHAMENEI.IR, Kharrazi ya ce, “Idan har aka yi shawarwari bisa tushe na hankali, kuma aka mutunta martabar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, to a shirye Iran take ta gudanar da shawarwari, kuma a shirye take ta tattauna, matukar dai an mutunta ka’idojin da suka dace, kuma ba a dora mata wata mummunar manufa ba, kuma idan har ana son dora mata wata mummunar manufa, to lallai za a fuskanci mayar da martaninta.”

Ya kara da cewa: “A cikin adabin siyasa, tattaunawa tana da ka’idoji, kuma tattaunawa mai daraja ita ce ta dogara da wadannan ka’idoji. Idan daya bangaren yana son yin amfani da karfi ko wata hanya don aiwatar da sakamakon shawarwarin, to wannan ba tattaunawa ce mai daraja ba wacce ta yi daidai da ka’idojin diflomasiyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted