Ma’aikatar huldar kasa da kasa da hadin gwiwa ta Afirka ta Kudu ta tabbatar da cewa: Tsagaita bude wuta a zirin Gaza ba zai kawar da laifukan da aka aikata kan fararen hula ba, tana mai jaddada cewa: Karar da aka shigar kan haramtacciyar kasar Isra’ila a gaban kotun kasa da kasa na da nufin hana sake aukuwar keta haddi, ba wai don dakatar da su na wani dan lokaci ba.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar Larabar da ta gabata ta ce: “Tsarin shari’ar ya nuna irin sadaukarwar da Afirka ta Kudu ta yi a tarihi wajen yakar wariyar launin fata da kuma kare hakkin al’ummar da ake zalunta,” yayin da ake ci gaba da shari’a kan haramtacciyar kasar Isra’ila kan aikata kisan kare dangi a Gaza.
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta jaddada aniyar ta na ci gaba da gudanar da shari’ar, duk da sanarwar tsagaita bude wuta tsakanin gwamnatin mamayar Isra’ila da bangarorin Falasdinu, la’akari da cewa adalcin kasa da kasa ba shi da alaka da abubuwan da ke faruwa nan take a kasa, sai dai a dora masu alhakin aikata manyan laifuka.
A watan Disambar shekara ta 2023 ne, Afirka ta Kudu ta shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa, inda ta zargi gwamnatin mamayar Isra’ila da yi wa fararen hula kisan kiyashi a zirin Gaza.