Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza

Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ce, fiye da Falasdinawa 35 ne su ka yi shahada daga Safiyar yau Laraba zuwa  tsakiyar rana,sanadiyyar hare-haren

Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ce, fiye da Falasdinawa 35 ne su ka yi shahada daga Safiyar yau Laraba zuwa  tsakiyar rana,sanadiyyar hare-haren da HKI take kai wa.

Hakan tana faruwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar  kiwon lafiya a Gaza ta yi gargadi akan cewa asibitocin yankin sun kusa daina aiki baki daya.

Tashar talabijin din ‘aljazira’ ta kasar Qatar ta ce,adadin wadanda su ka yi shahada har zuwa marecen yau sun kai 51,38 daga cikinsu a cikin birnin Gaza kadai.

A gefe daya rahoton tashar talbijin din ta ‘aljazira’ ya  bayyana cewa; HKI ta yanke hanyoyin sadarrwa na “Internet’ a fadin Gaza, haka nan kuma ta hana hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) shigar da makamashi cikin asibitocin yankin.

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gazan ta kuma ce, matukar ba a bari aka shigar da makamashi cikin asibitocin yankin ba, to komai zai tsaya.

A can yankin yammacin kogin Jordan kuwa, sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinawa 40 a garin ‘Assir” a yau Laraba kadai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted