Kasar Iran Ta Ce; Ta’addancin Isra’ila Kan Qatar Laifi Ne Da Ke Barazana Ga Tsaro Da Zaman Lafiya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan kasar Qatar laifi ne da ke barazana ga tsaro da zaman lafiya Jamhuriyar Musulunci

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan kasar Qatar laifi ne da ke barazana ga tsaro da zaman lafiya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kakkausar murya ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan kasar Qatar, tana mai jaddada cewa, harin da aka kai kan tawagar kungiyar Hamas da ke tattaunawa da kuma janyo shahadan Falasdinawa da ‘yan Qatar, babban laifi ne da kuma keta dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta jaddada cikakken goyon bayanta ga Doha wajen tunkarar wannan ta’addanci.

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana a cikin wata sanarwar da ta fitar cewa, wannan harin ta’addanci na nuni da cewa, cin zarafi ne da keta ka’idojin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya, da kuma ka’idojin dokokin kasa da kasa, gami da muzanta hurumin kasar Qatar a fili. An yi nuni da cewa, hakan na nuni da irin hatsari da ta’addancin yahudawan sahayoniyya yake da shi, wanda baya ga laifukan kisan kiyashi a Falastinu da ta mamaye, tana kuma kara fadada ayyukan wuce gona da iri a yankin baki daya, lamarin da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin da na kasa da kasa ta hanyar da ba a taba ganin irinsa ba.

Sanarwar ta jaddada cewa, Amurka da sauran kasashen da ke goyon bayan ‘yan sahayoniyya a siyasance, da kudi da kuma na soja, abokan tarayya ne a cikin laifuffukan wannan gwamnati, kuma wajibi ne su dauki nauyin wannan cin zarafi da keta haddi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted