Farkon Martanin Gwamnatin Siriya Kan Tofin Allah Tsinen Harin Da Isra’ila Ta Kai Kan Yankunan Kasarta

Martanin farko da gwamnatin Siriya ta fitar game da hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a Homs, Latakia da Palmyra Ma’aikatar harkokin wajen kasar

Martanin farko da gwamnatin Siriya ta fitar game da hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a Homs, Latakia da Palmyra

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Siriya ta yi kakkausar suka tare da Allah wadai kan hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu wurare a yankunan Homs, Latakia da Palmyra, lamarin da ya saba wa dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Siriya da kuma ‘yan kasashen ketare ta tabbatar da cewa: Wadannan hare-haren suna nuni ne a fili karara na keta hurumin Jamhuriyar Larabawa ta Siriya, barazana kai tsaye ga tsaronta da zaman lafiyar yankin, kuma wani bangare ne na ci gaba da kai hare-hare da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan yankunan Siriya.

A yayin da kasar Siriya ta yi kakkausar suka yi watsi da duk wani yunkuri na kawo cikas ga ikonta ko cutar da tsaron kasarta, tana kira ga kasashen duniya musamman kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya  da su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu na shari’a da da’a da kuma daukar kwararan matakai masu tsauri da zai kawo karshen wadannan hare-hare da ake ci gaba da yi da kuma tabbatar da mutunta ‘yancin kan kasar ta Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted