Iran, China da Rasha suna kan bakansu na kawo karshen kudiri mai lamba 2231 akan lokaci

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya gana da jami’an diflomasiyya na kasashen

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya gana da jami’an diflomasiyya na kasashen Sin da Rasha, game da yadda za a iya aiwatar da kudurorin yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya ce Iran, Rasha, da China sun yi imanin cewa kuduri mai lamba 2231 ya kamata ya kare a wa’adinsa, kuma kasashen Turai uku ba su da hurumin yin wani wajen wanann yarjejeniya.

Kazem Gharibabadi ya gana da jami’an diflomasiyya na China da Rasha game da hanyoyin da za a bi wajen tunkarar yarjejeniyar nukiliyar 2015.

Gharibabadi ya fada a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata cewa, ya gana tare da tuntubar wasu manyan jami’an diflomasiyyar Rasha da China a Tehran kan wannan batu.

Gharibabadi ya ce, “A ganawar da ya yi jakadan jamhuriyar  kasar Sin da jami’in ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha, mun tattauna tare da yin musanyar ra’ayi kan matakan hadin gwiwa don tinkarar barnar da gwamnatocin kasashen Turai uku suka yi kan kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2231.”

Ya kara da cewa, “Dukkan kasashen ukun sun yi imanin cewa ya kamata a kawo karshen  kuduri mai lamba 2231 a kan wa’adin sa, kuma wadannan kasashe uku na turai ba su da hurumin haifar da wata matsala kan hakan a kwamitin sulhu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments