Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zarge-zargen da Amurka da kasashen yamma suka yi mata Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya musanta zarge-zargen

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zarge-zargen da Amurka da kasashen yamma suka yi mata

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya musanta zarge-zargen da Amurka da Faransa da wasu kasashen yammacin Turai ke yi wa Iran a matsayin abin dariya da rashin tushe. Ya kuma jaddada cewa, suna daga cikin fito-na-fito na hasashe da kuma kokarin karkatar da ra’ayin jama’a daga muhimman batutuwan da ke faruwa a yanzu, wato kisan kiyashi da kashe-kashen jama’a da ake yi a kasar Falasdinu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya jaddada a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Juma’a cewa: Amurka, Faransa da dukkan sauran kasashen da suka sanya hannu kan sanarwar baya-bayan nan kan Iran, a matsayin gwamnatin da ke goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda da kuma karfafa tashin hankali, wajibi ne su dauki nauyin wadannan matakai da suka saba wa dokokin kasa da kasa.

Baqa’i ya yi tsokaci kan hare-haren wuce gona da iri da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka yi wa Iran a baya-bayan nan, da kuma laifukan kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a Gaza. Ya kuma jaddada cewa ana yin hakan ne tare da goyon baya ko amincewar wadanda suka rattaba hannu kan wannan bayani na adawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Iran

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted