Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi dirar mikiya kan Netanyahu a matsayin mai laifin yaki da ke ingiza Amurka kan yaki da Iran
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya soki fira ministan gwamnatin Isra’ila Benjamin Netanyahu, inda ya nuna shakku kan harkokin siyasarsa da kuma dangantakarsa da Amurka.
Yana tambayar cewa; Mene ne Netanyahu ke sha? Kuma mene ne hukumar leken asirin Mossad ta mallaka musamman a Fadar shugabancin Amurka ta White House?”.
A yayin da yake mayar da martani ga furucin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, Araghchi ya bayyana cewa; Netanyahu ya yi alkawarin nasara a Gaza kusan shekaru biyu da suka gabata, ya kara da cewa sakamakon da aka samu a matakin sojin ya zame sananne, inda Netanyahu yake fuskantar sammacin kamu kan laifukan yaki, da kuma amfani da matasa 200,000 a matsayin soji domin tunkarar kungiyar Hamas.
Dangane da shirin nukiliyar Iran kuwa, Araqchi ya ce: Netanyahu ya yi mafarkin ruguza nasarorin da aka cimma cikin shekaru 40 na ci gaban makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, yana mai cewa “kowanne daga cikin masana kimiyyar nukiliya 12 da sojojin hayarsa suka kashe, ya horar da kwararrun dalibai sama da 100 wadanda za su ci gaba da wannan tafiya.”
Ya kara da cewa ” Girman kai na Netanyahu bai tsaya nan ba, sai dai bayan ya kasa cimma manufofinsa kan Iran da kuma neman goyon bayan Amurka a lokacin da makami mai linzami na Iran ya lalata wuraren da aka mamaye a asirce, ya fara bayyana wa Amurka a fili abin da za ta ce da abin da za ta yi a tattaunawa da Iran.”
A karshe Araghchi ya yi nuni da cewa, hakikanin wauta ta gaskiya ita ce imanin cewa Iran za ta dauki duk wani bayani daga wani mai laifin yaki da ake nema ruwa a jallo zai yi.