Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin sharia da kuma kasa da kasa ya ce kasashe uku na turai Burtaniya da Faransa da kuma Jamus sun kada mutuncinsu a lokacinda suka giye bayan yakin kwanaki 12 wadanda HKI da Amurka suka dorawa JMI.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazen Gharibabadi yana fadar haka a hirar da yayi a wata tashar talabijan a nan Tehran a jiya Lahadi.
Jami’in diblomasiyyan ya kara da cewa wadannan kasashe uku sun gabatar da hujja marasa karfi a goyon bayan da suka bawa HKI da Amurka hujjar kaiwa Iran hare-hare. Kuma sune hujjojin da Amurkan da kuma HKI suka bayar a kwamitin tsaro na farwa kasar da yaki.
Kafin su fara yakin HKI da Amurka sun mika takardu wadanda a cikinsu suka shaidawa kwamatin tsaro na MDD kan cewa zasu fadawa Iran da yaki ne saboda hanata mallakar makaman Nukliya.
Yace: Gwamnatin kasar Iran tana da yencin maida martani a kan wadannan kasashe guda biyu. Banda wadannan kasashe uku, babuwata kasar turai da ta goyi bayan HKI a yakin.