Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake Sarrafa Shi Daga Nesa Na 19

Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa samfurin MQ-9 na 19 a jiya Lahadi da yamma a sararin samaniyar

Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa samfurin MQ-9 na 19 a jiya Lahadi da yamma a sararin samaniyar kasar.

Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ya bayyana cewa sojojin kasar ta Yemen sashen UAV wato masu kula da abinda ake kira ‘Drones’ sun bada sanarwan kakkabo jirgin yaki na Amurka ne a lokacinda yake tattara bayanai a wasu yankuna a sararin samaniyar kasar.

Masana sun bayyana cewa farashin ko wane jirgi yakin samfurin MQ-9 ya kai dalar Amurka miliyon $33, don haka ya zuwa yanzu kasar Amurka ta yi asarar dalar Amurka miliyon $600.  Kafin haka dai sojojin Yemen bangaren makamai masu linzami sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami samfurin Balistic  guda biyu kan HKI, wanda ya kai ga rufe tashar jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv.) . Bugediya Yahyah Saree kakakin sojojin kasar ta Yemen ya bayyana cewa godiya ta tabbata ga All..saboda dukkan makaman sun cimma manufofin cillasu, wadanda suka hada da rufe tashar jiragen sama na Bengrion da tilastawa miliyoyin yahudawan sahyoniyya gudu zuwa wuraren buya.

Saree ya kammala da cewa, ayyukan soje a kan HKI da kuma Amurka zasu ci gaba har zuwa dakatar da yaki a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments