Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar  Makamashin Nukiliya Ta Iran

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran.

Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa:  Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage.

Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments