UNICEF: Yara a Gaza suna fama da matsalar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba a kan kananan yara.

“Ba mu da wani bayani a tarihin wannan zamani dangane da ke bukatar tallafin lafiyar kwakwalwa kamar yaran Gaza,” in ji mai magana da yawun UNICEF James Elder a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva.

Sannan kuma jami’in  ya yi Allah wadai da tauye hakkin yara da ake yi da gangan a Gaza, ya kuma bukaci masu karfin fada a ji a duniya da su dauki mataki.

Ya kara da cewa an toshe alluran rigakafi 180,000 na rigakafin yara masu mahimmanci, da na’urorin saka jariran da ba su kai ga lokacin haihuwa ba, inda Isra’ila ta hana shigar da wadannan kayayyakia  cikin yankunan zirin gaza.

Babban jami’in na UNICEF ya ce, daukar irin wadannan matakana  kan yara yana a matsayin babban laifi wanda ka iya zama laifin yaki bisa dokoki na kasa d akasa.

A kan haka ya kara jaddada kiransa ga kasashe masu karfin fada a ji da su sauke nauyin da ya rataya a kansu kan batun Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments