Kasashen Iran da kuma Rasha zasu kamala cikakiyar yarjejeniyar dake a tsakaninsu nan ba da jimawa ba.
Wannan bayyanin ya fito ne ta bakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov wanda ya ce Rasha za ta kammala cikakkiyar yarjejeniya tsakaninta da Iran “nan gaba kadan.”
Lavrov ya ce kasashen biyu “za su kulla sabuwar yarjejeniya ta hadin gwiwa a tsakaninsu.
Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da dalibai da malamai na Cibiyar Hulda da Kasa da Kasa ta Jihar Moscow (MGIMO) a ranar Litinin.
Lavrov ya ce yarjejeniyar zata kasance wani mataki na inganta dangantakar Tehran da Moscow bayan zuwan sabuwar gwamnatin Iran a karshen watan Yuli.
Babban jami’in diflomasiyyar na Rasha ya bayyana kwarin gwiwa cewa kalaman sabon shugaban kasar Iran da ministan harkokin wajen Iran game da ci gaba da huldar da ke tsakanin su “yana nuna kyakkyawar manufa na sabuwar gwamnati a Iran.
Idan za’a iya tunawa, Iran da Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta shekaru 10 da aka tsawaita zuwa shekaru 20.