An bayyana marigayi Imam Khumaini (r.a) a matsayin tushen samar da nasarorin da gwagwarmaya take samu a wannan zamani
Manazarta da masharhanta sun bayyana cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila sun hana batun ambaton matsalolin al’ummar Falastinu, da hana batun tunasar da hakkokin Falasdinawa a tsakanin al’ummar Larabawa da Musulmi, amma zuwa Imam Khumaini {r.a} ya kawar da batun Falastinu daga kuntataccen kangin da aka killace shi zuwa faffadan batu da ya shafi al’ummar musulmi tare da dasa karfin gwiwa da ruhin nasara a zukatan matasa kan ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya da karyar babakeren Amurka kan lamarin na Falasdinawa, tare da karfafa ruhin gwagwarmaya da makami domin kwato ‘yanci da hakkoki lamarin da ya karfafa ruhin ‘yan gwagwarmaya wajen tunkarar ‘yan mamaya.
Wannan zurfin tunani na Imam Khumaini {r.a} ya ci gaba da wanzuwa har zuwa yanzu, inda a ‘yan kwanakin nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki nauyin gudanar da zaman taron kasa da kasa kan tunasar da mummunan halin da al’ummar Gaza suke ciki, inda zaman taron ya samu halartar manyan jami’an siyasa daga kasashen duniya daban-daban, kuma aka tattauna batutuwa da suka shafi matsalolin Falasdinu da hanyoyin kalubalantar ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya gami da tunanin rusa shirin Amurka na dasa babakere ‘yan sahayoniyya a yankin gabas ta tsakiya.