Gidan radiyon sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya watsa labarin cewa: Shiyar arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba da konewa sakamakon luguden wutar kungiyar Hizbullah ta Lebanon
Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta tilastawa yahudawan ‘yan kaka gida kimanin 100,000 tserewa daga matsugunansu sakamakon luguden wuta da makamai masu linzami da ta yi kan wasu manyan matsugunai a yankin Khalil mai nisa da kuma yankin Julan na Siriya da aka mamaye, lamarin da ya yi sanadin tashin gobara mai tsanani a yankunan da aka kai hare-haren. Kamar yadda hare-haren na Hizbullahi suka ruguza cibiyar kariya ta sararin samaniya na “Iron Dome” mallakin yahudawan sahayoniyya da ke yankin na Julan da aka mamaye.
Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Yahudawan Sahayoniyya ‘yan kaka gida kimanin 100,000 ne suka tsere daga matsugunansu zuwa maboyar karkashin kasa bayan da aka kunna kararrawar gargadi, sannan wasu jiragen sama marasa matuka ciki biyu makare da bama-bamai biyu sun tarwatse a matsugunan yahudawa na Nahariya da Akka, ba tare da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun samu nasarar kakkabo su ba kafin kai hare-haren.