Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyukan Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya

 Rahotanni sun nuna cewa tsohon ministan harkokin wajen kasar iran mohammad Javad zarif yace isra’ila ce kawai gwamnatin dake ayyukan nukiliya ba bisa kaida ba

 Rahotanni sun nuna cewa tsohon ministan harkokin wajen kasar iran mohammad Javad zarif yace isra’ila ce kawai gwamnatin dake ayyukan nukiliya ba bisa kaida ba a yammancin asiya, amma take sukar iran duk da cikakken hadinkai da take bayarwa ga dokokin hukumar nukiliya kuma wadda ke da tarihi mafi girma na binciken hukumar nukiliya ta duniya,

Zarifi ya fadi haka ne a wajen taron international iranology da aka gudanar a birnin Tehran, kuma ya bayyana matsayin iran na dogon lokaci inda isra’ila take kokarin haifar da barazana a yankin domin kawar da kokarin deiplomasiya da ake yi na yarjejeniyar JCPOA.

Har ila yau ya jaddada cewa batun danganta shirin iran da barazanar tsaro wani makirci ne da aka kulla domin jefa yankin cikin rikici.

Daga karshe ya ce iran kowanne lokaci tana nan akan bakkanta na tattaunawa, amma ba zata mika wuya ga duk wata barazana ba,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments