Search
Close this search box.

Zanga-Zangar Yahudawan Sahayoniyya Na Neman Kullar Yarjejeniyar Sakin ‘Yan Uwansu

Yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da gudanar da zanga-zanga a haramtacciyar kasar Isra’ila lamarin da ya wurga Netanyahu cikin tsaka mai wuya Rahotonni sun bayyana

Yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da gudanar da zanga-zanga a haramtacciyar kasar Isra’ila lamarin da ya wurga Netanyahu cikin tsaka mai wuya

Rahotonni sun bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya masu zanga-zanga sun rufe wata babbar hanya da ke tsakiyar birnin Tel Aviv a korafin da suke yi na neman kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da gwagwarmayar Falasdinawa domin sakin ‘yan uwansu da ake tsare da su a hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa a matsayin fursunonin yaki.

Iyalan fursunonin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kuma bukaci a kawo karshen yakin da gwamnatin Netenyahu ta daura kan Zirin Gaza tare da hanzarta kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da gwagwarmayar Falasdinawa da za ta mayar da dukkan ‘ya’yansu gida, a cikin wata sanarwa da suka fitar a gaban hedikwatar Ma’aikatar Yakin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila, kamar yadda suke rera taken cewa; Ci gaba da yakin zai haifar da hasarar rayuka a tsakanin fursunonin da ake tsare da su da kuma sojojin da suka tafi yakin, don haka suke zargin gwamnatin Netanyahu da daukan nauyin hasarar rayukan da ake yi a Gaza, kuma sun jaddada korafin cewa; Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta wurga ‘ya’yansu cikin hatsarin mutuwa, don haka suke neman ceto wadanda ake tsare da su daga masu rai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments