Fira ministan HKI Benjamin natanyaho ya bukaci yafiyar shugaban kasa game da shari’a da aka dade ana yi kan zargin da ake masa na cin hancin da rashawa da mutane da sauran yan siyasa ke Allah wadarai da shi.
Mazu zanga zanga sun mamaye gidan shugaban gwamnatin isra’ila Isaac Herzog inda suka yi tir da wanna mataki kuma suka bayyana shi a matsayin keta doka , suna ta daga ganyen Ayaba da aciki aka rubuta afuwa, wanda ke kwatanta wani shiri ne na jamhuriyar ayaba.
Natanyaho mai shekaru 76 da haihuwa ya nemi afuwar shugaba Herzog a hukumance yana kokarin tsrewa daga gidan kaso idan aka yanke masa hukumci, shekaru da yawa ke nan natanyaho yake neman afuwa kamar yadda dokokin isra’ila suka bukaci ya amince da laifukansa.
Manyan yan adawa sun hade kansu wajen neman shugaban kasar yayi watsi da bukatarsa, sai dai idan natanyaho ya cika sharudda guda biyu masu tsauri ya amince da laifukan da ya aikata kuma ya fice daga harkokin siyasa na har abada.