Al’ummar Libiya sun fito gagarumar zanga-zangar a birnin Tripoli bayan bayyanan shirye-shiryen ganawar tsohuwar ministar harkokin wajen Libiya da takwaranta na haramtacciyar kasar Isra’ila
Babban birnin kasar Libya, Tripoli, ya fuskanci gagarumar zanga-zanga bayan wata sanarwa da tsohuwar ministar kasar Najla Al-Mangoush ta fitar cewa: Hakika ta amince da cewa; Fira ministan gwamnatin hadin kan kasa shi ne ya amince da shirin ganawarta da tsohon ministan harkokin wajen gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Eli Cohen.
Jaridar Russia Today na kasar Rasha ta watsa rahoton cewa: Mazauna karamar hukumar Souq al-Juma da ke babban birnin kasar Tripoli sun kona tayoyi tare da rufe muhimmiyar hanyar Shatt da ke birnin Tripoli domin nuna adawa da duk wani Shirin kyautata alaka tsakanin kasar LIbiya da haramtacciyar kasar Isra’ila. Wannan yunkuri ya zo ne bayan da tsohuwar ministar harkokin wajen Libiya Najla al-Mangoush, ta yi furuci da cewa: Fira ministan gwamnatin rikon kwaryar kasar ne Abdul Hamid Dabaiba, shi ne ya jagoranci shirya zaman ganawarta da tsohon ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Eli Cohen a shekara ta 2023.
Masu zanga-zangar sun bukaci “kifar da gwamnatin Abdul-Hamid Al-Dabaiba bayan da Al-Mangoush ta fasa kwai kan ganawar da ta yi da takwararta na haramtaciyar kasar bisa tsarin gwamnatin Libiya karkashin jagorancin gwamnatin hadin kan kasa.