A gobe Litinin 24 ga watan Maris ne tawagogin masu tattaunawa na kasashen Amurka da Rasha zasu hadu a birnin Rayida na kasar Saudiya don ci gaba da tattaunawan da suka fara a yan makonnin da suka gabata dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine, shekaru fiye da 3 da suka gabata, da kuma dangantaka a tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto Yury Ushakov mai bawa shugaba Putin shawara kan al-amurin siyasa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa Sanata Georgy Karasin ne zai jagoranci tawagar masu tattaunawa ta kasar Rasha sannan ta kasar Amurka an rika an samar da tawagar, wasu zata hadu da na Rasga a gobe litin a birnin Riyad.
Kafin haka dai shugaban kasar Rasha Vladimir Putin sun tattauna da tokwaransa na kasar Amurka Donal Trump kan al-amura da dama wadanda suka shafi yakin a Ukraine da tsagaita budewa juna wuta na wata guda da kuma wasu al-amura.
Karsin daga karshe ya ce yana fatan tattaunawan zata yi armashi.