Yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da yin kutse cikin Masallacin Al-Aqsa, yayin da kungiyar Hamas ta yi kira da a kalubalance su
Daruruwan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida a safiyar yau Alhamis suka kutsa cikin harabar Masallacin Al-Aqsa, karkashin kariyar da ‘yan sandan gwamnatin mamayar Isra’ila, yayin da ake ci gaba da kiraye-kirayen gudanar da taron gangami da kuma jaddada rashin amincewa da keta hurumin alkiblar musulmi na farko, kuma daya daga cikin Masallatai masu daraja na al’ummar musulmin duniya.
Majiyoyin daga Qudus sun ba da rahoton cewa: Tsagerun yahudawan sahayoniyya mazauna matsugunai da dama sun gudanar da rangadi masu tayar da hankali a harabar Masallacin Al-Aqsa mai albarka, ciki har da gudanar da ibadar Talmud da raye-rayen neman tsokana.