Dakarun Yeman sun sanar da sake kai hari kan filin jirgin saman Isra’ila na Ben Gurion da ke kusa da birnin Tel Aviv da makami mai linzami mai linzami.
Bayanai sun ce ko wannan karo tsarin garkuwa daga hare haren sama na Amurka samfarin THAAD ya gaza kakkabo harin.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta Birgediya Janar Yahya Saree ta bayyana cewa, an kai harin ne yau Juma’a.
Kakakin rundunar ‘yan Houthi Yahya Saree ya ce, sun yi amfani da makami mai linzami mai gudun tsiya,”
Isra’ila dai ta sha alwashin mayar da martani mai karfi kan harin.
Kasar Yemen dai na mai kai hari kan kaddarorin Isra’ila domin nuna goyan baya ga al’ummar Gaza da ke fuskantar hare-hare daga Isra’ila.