Kasar Yemen ta jaddada cewa: Ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai munanan hare-hare kan Amurka idan ta dawo da kai hari a kan kasarta
Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji guda uku kan tashar jiragen sama na Ramon, wani muhimmin wuri ne na makiya yahudawan sahayoniyya, da a wurin akwai jirgin ruwan Amurka Truman mai dauke da dauke da jiragen saman yakin Amurka da kuma wasu kayayyakin yakinta.
Majiyar sojojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sojojin samanta sun gudanar da ayyukan soji guda biyu, na farko a kan filin jirgin saman “Ramon” na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Umm al-Rashrash a kudancin kasar Falasdinu da aka mamaye da jiragen sama masu saukar ungulu guda biyu, yayin da hari na biyun an kai harin ne kan wani muhimmin yanki a Jaffa da aka mamaye da wani jirgin sama maras matuki ciki, nau’in “Jaffa”, don tallafawa al’ummar Falastinu da ake zalunta.
A cikin wata sanarwa da kakakinta Birgediya Janar Yahya Sari’e ya fitar ya tabbatar da cewa: “A cikin yanayin tunkarar hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen da kuma mayar da martani kan laifukan da suke yi kan al’ummar kasar, sojojin ruwa da na sama sun gudanar da wani farmaki na musamman na soji kan jirgin Amurka Truman da kuma wani adadi mai yawa na jiragen yakinta a tekun Bahar Maliya da wani makami mai linzami.”