Kasar Yemen ta gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan fuskantar hare-hare masu zafi idan har ta karya yarjejeniyar Gaza
A ranar Lahadin da ta gabata, Hazam al-Assad, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullahi ta Yemen, ya gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan karin fuskantar hare-hare masu zafi idan ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
A wata sanarwa da ya fitar ta hanyar gidan radiyo Sputnik ta kasar Rasha, Hazam al-Assad ya tabbatar da cewa: Yemen za ta dakatar da kai hare-hare kan gwamnatin mamayar Isra’ila, idan har ta yi aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza.
Tun da farko dai shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila da kungiyar Hamas sun rattaba hannu kan matakin farko na shirinsa na zaman lafiya.
A nata bangaren, Kungiyar Hamas ta sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza, wadda ta hada da shigar da kayan agaji da musayar fursunoni. Ta yi kira ga shugaban kasar Amurka Donald Trump da kasashen da suka amince da yarjejeniyar, da kuma kasashen Larabawa, da na Musulunci, da na kasa da kasa, da su tilastawa haramtacciyar kasar Isra’ila aiwatar da yarjejeniyar gaba daya.
A yau litinin ne za a gudanar da shawarwarin a Sharm el-Sheikh a birnin Alkahira, tare da halartar shugaban Amurka Donald Trump da kasashe masu shiga tsakani, domin kafa dukkanin sharuddan da suka dace domin samun nasara da kuma ci gaba da aiwatar da shirin, wanda bangarorin Falasdinu da gwamnatin mamayar Isra’ila suka amince da shi.