Majiyar gwamnatin kasar Yemen ta basa sanarwan kai hare-hare har sau biyu kan kataparen jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki na kasar Amurka dake cikin Tekun Red sea, wato USS Harry Truman. Inda suka cilla makami mai linzami guda da kuma jiragen yake wadanda ake sarrafasu daga nesa kan jirgin.
Har’ila yau sojojin yamen sun ce sun kaiwa wasu sojojin Amurka hare-hare da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa duk a cikin sa’oi 48 da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Yahyah Saree ya na fadar haka a safiyar yau talata, ya kuma kara da cewa sojojin kasar za su ci gaba da maida martani da kuma hana jiragen ruwan kasashen da take gaba da su a tekun maliya.