Yemen Ta Ce Ta Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Samfurin F18 A Kan Tekun Maliya, Amma Amurka Ta Musanta Hakan

Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta bayyana cewa ta sami sabbin makamai wadanda a halin yanzu suke iya kakkabo manya-manyan jiragen saman yaki na Amurka

Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta bayyana cewa ta sami sabbin makamai wadanda a halin yanzu suke iya kakkabo manya-manyan jiragen saman yaki na Amurka da HKI a yakin da suke fafatwa da su dangane da yaki a Gaza.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar gwamnatin kasar Yemen na cewa jiragen yakin Amurka da Burtaniya sun kai hare-hare a jihar Hudaida da kuma San’aa babban birnin kasar, sannan sojojin kasar na Yemen sun maida martani da makaman kakkabo jiragen sama yaki, kuma sun sami nasarar kakkabo jirgin saman yaki na Amurka samfurin F18 wanda ya fadi a cikin tekun (Red Sea) ko tekun Maliya.

Sun ce jirgin ya tashi ne daga kataparen jirgin yaki mai daukar jiragen sama na Amurka wanda ake kira (Carrie ) a yankin.

Amma hukuma mai kula da al-amuran yaki a nahiyar Asia ta kasar Amurka CENTCON ya bayyana cewa jirgin ya fadine tare da makaman kawayenta ko kanta saboda kuskure.

Labarin yakara da cewa matuka jirgin guda biyu duk sun  tsari ba tare da wata cutarwa na a zo a gani ba.

Ansarallah ta kasar Yemen dai ta bayyana cewa yakinsu da HKI zai ci gaba, har zawa lokacinda za’a kawo karshen yaki a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments