Yemen: Ansarallah Ta Yi Kira Ga Hadin Kan Musulmi, Don Kawo Karshen Yaki A Gaza

Miliyoyin mutanen kasar Yemen sun fito zuwa dandalin taron mutane a dukkan garuwan kasar a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar manzon All…(s) a kasar a

Miliyoyin mutanen kasar Yemen sun fito zuwa dandalin taron mutane a dukkan garuwan kasar a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar manzon All…(s) a kasar a jiya Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sayyeed Abdulmalik al-houthi, a jawabin da ya gabatar a karshen tarurrukan, zuwa ga hadin kan kasashen musulmi saboda ma’abucin wannan ranar (s).

Ya kuma yi tir da allawadai da ci gaba da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza. Ya kuma yi addu’a ga shahidan gwamnatin kasar wadanda HKI ta kashe a makon da ya gabata. Har’ila yau a cikin Jawabinsa Sayyid Huthi ya bayyana cewa, mutanen yemen da yardarm All..suna daga cikin wadanda suke raya addinin musulunci bayan rauninsa. Sannan daga cikin ayyukan raya wannan addinin akwai raya wannan ranar ta haihuwar manzon All…(s) da kuma tsayin dakan da suka yi wajen tallafawa al-ummar Falasdinu. Daga karshe sayyeed Huthi ya bayyana cewa, abinda ke faruwa a Gaza, wanda ya hada da hana jarirai madaran sha, yayi muni, kuma yakamata ya tada hankalin dukkan mutane wadanda suke da yan’adamtaka gwagwadon kwayan zirra a cikin zukatansu. Ya kuma yi tir da HKI a kan ta’asan da take aikatawa a ko wace rana a yankin yamma da kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments