Yemen: An Harbo Jirgin Saman Amurka  Samfurin MQ9

Rahotanni daga kasar Yemen sun ce an harbo jirgin saman maras matuki na Amurka samfurin MQ9 ne a yankin Sa’adha da safiyar yau. Gabanin wannan

Rahotanni daga kasar Yemen sun ce an harbo jirgin saman maras matuki na Amurka samfurin MQ9 ne a yankin Sa’adha da safiyar yau.

Gabanin wannan lokacin dai sojojin na kasar Yemen sun harbo jiragen Amruka marasa matuki, musamman samfurin MQ9 wanda shi ne na koli a jerin jiragen Amurka na leken asiri.

Sojojin na kasar Yemen dai suna fuskantar hare-hare daga jiragen yakin Amurka da Birtaniya, saboda shigarsu cikin masu taimakawa Falasdinawa ta hanyar hana jiragen ruwa zuwa HKI.

 Sojojin na Yemen dai sun sanar da cewa, sai idan an kawo karshen yakin Gaza sannan ne za su daina tare jiragen ruwa  da suke zuwa HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments