Shugaban rundunar kare juyin juya halin musulunci a nan Iran IRGC, wato Janar Hussain Salami ya yi kira ga kasashen musulmi su rufe dukkan hanyoyin tallafawa HKI saboda kisan kiyashin da takewa Falasdinawa.
Tashar talabijin ta PressTv a nan Tehran ta nakalto Janar Salami yana fadar haka a yau Jumma’a, ya kuma kara da cewa sammacin kama firai ministan HKI wanda kotun ICC ta yi wata nasarace babba ga Falasdinawa da kuma mutanen kasar Lebanon, har’ila yau da kuma wadanda suke goyon bayansu a duniya.
Salami ya kammala da cewa wannan hukuncin da kotun ICC ta fitar a jiya ya nuna karshen siyasar HKI a duniya Kenan. Daga yanzun kuma babu jami’in gwamnatin wata kasa da zata je HKI sai Amurka wacce ta kasance babbar kasa mai goyon bayan haramtacciyar kasar a duniya.