Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata cewa adadin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata tun ranar 18 ga Maris, shekara ta 2025 ya kai shahidai 1,890 da kuma jikkata wasu 4,950 na daban.
An tabbatar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a sakamakon harin ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa shahidai 51,266 da jikkatan wasu 116,991 tun daga ranar 7 ga Oktoban shekara ta 2023.