Yara Kimani 100 Ne Suka Mutu A Gaza Tun Lokacinda Aka Tsagaita Bude Wuta

Yara 6 ne suka mutu saboda tsananin sanyi a gaza a wannan fasalin sanyan, inji hukumar UNICEF mai kula da yara ta MDD a Gaza.

Yara 6 ne suka mutu saboda tsananin sanyi a gaza a wannan fasalin sanyan, inji hukumar UNICEF mai kula da yara ta MDD a Gaza.

Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta nakalto kakakin hukumar James Elder yana fadawa yan jarida a birnin Geneva  a yau Talata hakan. Ya kuma kara da cewa;  duk tare da tsagaita wuta a Gaza a cikin watan Octoban da ya gabata, ya rage yawan mutanen da HKI take kashewa a gaza, amma yara basu daina mutuwa ba, saboda a lissafin hukumar tun bayan tsagaita wuta: yara kimani 100 ne sojojin HKI sukakashe a Gaza.

Elder ta kara da cewa yara a gaza suna mutuwa hatta bayan tsagaita wuta da hare-haren jiragen yaki wani lokaci, ko aman wutan tankunan yaku, hare-haren jiragen Drons wadanda ake sarrafasu daga nesa, wani lokacin kuma da bindigan sojojin HKI kai tsaye a kan su.

A wani bangaren kuma kungiyar bada agaji ta fararen hula a Gaza ta bada sanarwan cewa mutane 31 sanyi ta kashe a gaza tun bayan shigowar fasalin sanyi da ruwan sama a gaza, a dai dai lokacinda hki take ci gaba da hana shigowar kayakin agaji zuwa cikin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted