‘Yan Tawayen Syria Masu Iko Da Kasar Sun Sha Alwashin Hana Kaiwa Isra’ila Hari Daga Cikin Kasar

Shugaban kungiyar ta Hayat Tahrir al-Sham ko kuma Nusra Front a baya, reshen kungiyar Alka’ida a Syria da ke dauke da makamai da ake kira

Shugaban kungiyar ta Hayat Tahrir al-Sham ko kuma Nusra Front a baya, reshen kungiyar Alka’ida a Syria da ke dauke da makamai da ake kira da ‘yan tawayen Syria, da a halin yanzu suka kwace iko da kasar, ya bayyana cewa ko alama ba za su taba bari a yi amfani da kasar Syria wajen kai wa Isra’ila hare-hare ba.

Shuban Tahrir Sham, Aljolani Ya ce; Ba ma son duk wani rikici da Isra’ila kuma  ba za mu bari a yi amfani da Syria a matsayin hanyar kaddamar da hare-hare a kanta ba, kamar yadda ya sheda wa jaridar Times a wannan Litinin.

Yaki ya bayyana matsayarsu kan yadda za su tunkari hare-haren Isra’ila a kan Syria, da kuma ci gaba da mamaye yankunan kasar Syria da take yi tun daga ranar da suka sanar da kwace gwamnati a Syria.

Tun da farko dai Jolani  ya tabbatar da cewa kungiyarsa “ba za ta shiga cikin rikici da Isra’ila ba, yana bayyana cewa tsohuwar gwamnatin Syria da Iran da kuma Hizbullah ne kawai suke da matsala da Isra’ila , kuma a halin yanzu basu da samu a cikin kasar Syria.

Tsohon shugaban reshen kungiyar Al-Qaeda a Syria kuma tsohon mataimakin kwamandan Daesh (ISIS) da ke rike da ragamar iko a Syria a halin yanzu ya jaddada cewa, babbar matsalarsua  yanzu ita ce Hizbullah da Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments