‘Yan Tawayen Sudan Sun Kona Wani Bangaren Matatar Mai Ta Al-Jili Da Ke Birnin Khartoum Bahri

Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Kungiyar Rapid Support Forces sun kai hari kan matatar mai ta Al-Jili da ke birnin Khartoum na kasar Sudan Mayakan

Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Kungiyar Rapid Support Forces sun kai hari kan matatar mai ta Al-Jili da ke birnin Khartoum na kasar Sudan

Mayakan kungiyar dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan matatar mai ta Al-Jili da ke birnin Khartoum Bahri, wadda ita ce matatar mai mafi girma a kasar Sudan, wadda take samar da man fetur a yawancin jihohin kasar ta Sudan, duk kuwa da cewa kwararru sun tabbatar da takaitar barnar da aka yi wa matatar Man duk da tashin bam da aka samu a cikin matata da ya tilasta dakatar da duk wani aiki a cikinsa.

Sojojin Sudan sun yi amfani da dama a lokacin da dakarun kungiyar Rapid Support Forces suke fita daga matatar man, zuwa shiyar lardin Darfur domin neman mafaka mafi aminci, inda sojojin suka yi musu luguden bama-bamai ta hanyar jiragen saman yaki, wasu rahotonni suna cewa; Har yanzu Dakarun kai daukin gaggawan ne suke iko da mafi yawan jihohin lardin Darfur da ke arewacin kasar ta Sudan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments