“Yan Ta’addan Syria Suna Boye Gawawwakin Mutanen Da Su Ka Yi Wa Kisan Gilla

Rahotannin da suke fitowa daga Syria sun ambaci cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke da alaka da shugaban gwamnatin Syria, Julani sun fara dauke gawawwakin

Rahotannin da suke fitowa daga Syria sun ambaci cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke da alaka da shugaban gwamnatin Syria, Julani sun fara dauke gawawwakin mutanen da su ka yi wa kisan kiyashi zuwa wasu wurare da ba a san ko’ina ne ba.

Saboda yadda fushin kasashen duniya yake karuwa akan kisan kiyashin da ‘yan ta’adda su ka yi a gabar ruwan Syria, masu mulki a Damascuss suna boye gawawwakin gabanin isar tawagar MDD zuwa yankin.

Mafi yawancin mutanen da aka yi wa kisan gillar a yankin gabar ruwan Syria, fararen hula ne wadanda aka fito da su daga cikin gidajensu,yayin da wasu kuma aka yi musu kisan gilla a gaban iyalansu.

Ya zuwa shekaran jiya ana maganar cewa an kashe mutanen da sun kai 1,700.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments