Search
Close this search box.

Yan Nijeriya fiye da miliyan 31 na fama da ‘matsanancin’ Karancin abinci

Fiye da ‘yan Nijeriya miliyan 31.8 ne suke cikin mawuyacin yanayi na ƙarancin abinci, sakamakon ƙalubalen tsaro da kuma cire tallafin man fetur, kamar yadda

Fiye da ‘yan Nijeriya miliyan 31.8 ne suke cikin mawuyacin yanayi na ƙarancin abinci, sakamakon ƙalubalen tsaro da kuma cire tallafin man fetur, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana a ranar Talata tana mai nuni da wani bincike da wasu abokan hulɗarta daga ƙasashen duniya suka gudanar.

Matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ta fi ƙamari a tsakanin mata da ƙananan yara, a cewar binciken da aka gabatar a wani taro na gwamnati a ranar Litinin da Talata, a cewar da sanarwar Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare ta ƙasar ta bayyana.

Sakamakon binciken ya nuna cewa an samu ƙarin mutane miliyan 18.6 waɗanda Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa suna fama matsanancin ƙarancin abinci daga watan Oktoba zuwa Disamba na 2023.

”Hauhawar farashin kayayyakin abinci, sakamakon cire tallafin man fetur da kuma matsalar tsaro sun yi sanadin jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin yanayi,” in ji Ma’aikatar.

Hare-haren ‘yan ta’adda masu ɗauke da makamai sun tilasta wa miliyoyin manoma ƙaurace wa gonakinsu, lamarin da ya ƙara rura matsalar ƙaranci da kuma tsadar abinci a ƙasar.

Shugaba Bola Tinubu, wanda ya hau mulki a watan Mayun 2023, ya cire tallafin man fetur ne domin rage yawan kuɗaɗen da gwamnati take kashewa, lamarin da ya ta’azzara yanayin tsadar rayuwa da ake ciki a ƙasar.

Hukumomin samar da ci gaba waɗanda suka haɗa da Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya tare da Ƙungiyar Haɗin Gwiwa ta samar da abinci mai gina jiki da kuma Hukumar Samar da ci Gaba ta Jamus GIZ ne suka gudanar da wannan bincike.

Binciken ya yi amfani da ƙididdiga da aka samu daga ƙungiyar da ke samar da bayanai kan abinci mai gina jiki ta Cadre Harmonise.

Sanjo Faniran, babban mai kula da tsarin samar da abinci a Nijeriya sannan Daraktan ci gaban zamantakewa a Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, ya ce binciken ya taimaka wajen gano giɓin da ake da shi da kuma nasarori da ƙalubale tare da bayar da shawarwari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments