Tashar talabijin ta 13: ta bayar da labarin cewa; Makamai masu linzamin da aka harba wa Isra’ila daga yankin Beit-Hanun sun zama abin mamaki, saboda sojojin Isra’ilan sun sha mai wa yankin hare-hare.
Kafafen watsa labarun na HKI sun ce, Da alama Hamas tana da makamai masu linzami da dama da idan ta harba su za su isa birnin Tel Aviv.
“Yan gwgwarmayar sun harba makami mai linzamin ne daga kusa da inda sojojin mamayar suke a girke.