Kakakin rundunar Izzuddeen –Al-Qassam ya ce: A shirye suke su ci gaba da dogon yaki da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila
Abu Ubaida, kakakin rundunar Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ya bayyana cewa: Bayan makwanni 32 da fara yaki tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, al’ummar Gaza da ‘yan gwagwarmayarta suna ci gaba da yin tsayin daka a yakin da suke yi da ‘yan mamaya. Abu Ubaida ya kara da cewa: A tsawon kwanaki da darare da kuma makonni, makiya da gwamnatinsu ‘yan Nazi suna ci gaba da aiwatar da munanan laifukan kisan kiyashi a kan al’ummar Falasdinu.